Skip to main content

Posts

Entry and Exit Trigger

 Entry and Exit Triggers a Kasuwar Crypto Trading A kasuwar crypto trading, sanin entry da exit triggers yana da matukar muhimmanci don cin moriyar kasuwa ba tare da fadawa cikin asara ba. Entry trigger yana nufin lokacin da ya dace ka shiga kasuwa, yayin da exit trigger ke nufin lokacin da ya dace ka fita daga kasuwa don riba ko rage asara. Entry Triggers (Shiga Kasuwa) Entry trigger yana taimakawa wajen tabbatar da cewa ka shiga kasuwa a lokacin da ya dace. Ga wasu daga cikin abubuwan da za ka iya amfani da su don yanke shawarar shiga: 1. Technical Indicators Moving Averages (MA): Idan farashin ya keta sama da Moving Average (kamar 50 EMA ko 200 EMA), yana iya zama alamar bullish entry. Relative Strength Index (RSI): Idan RSI ya yi ƙasa da 30, yana iya nuna cewa kasuwa ta yi oversold kuma yana yiwuwa farashin ya tashi. MACD Crossover: Idan MACD line ya haye sama da signal line, yana iya nuna bullish entry. 2. Chart Patterns Breakout: Idan farashin ya karya wani key resistance lev...

WEB 3 opportunities

 Damar Makin Dake Cikin Web3 A yau, duniya na tunkarar sabon salo ta fuskar fasaha da tattalin arziki ta hanyar Web3 — wani sabon tsarin yanar gizo da ke amfani da fasahar blockchain don kawo cin gashin kai, tsaro, da gaskiya. A cikin wannan sabon yanayi, dama ta musamman ta bayyana a fannonin kasuwanci, aikin yi, da kirkire-kirkire. Ga wasu daga cikin damar makin da ke akwai: 1. Ciniki da Zuba Jari a Crypto Web3 ta bude kofa ga sababbin hanyoyin zuba jari kamar su: Futures Trading: Yin hasashen hauhawa ko faduwar darajar coins. Staking da Liquidity Providing: Samun riba ta hanyar bada gudummawa wajen tabbatar da amincin hanyoyin blockchain. 2. Content Creation Content creators suna da damar samar da content mai amfani kamar: Education: Bayar da ilimi akan amfani da crypto da dApps. NFTs: Samar da fasahohin dijital da za a iya siyarwa ko musayar su. 3. Kasuwanci da Cinikayya Akwai damar kafa kasuwanci da dama, irinsu: DeFi (Decentralized Finance): Bada lamuni ko karbar lamuni ba ta...

Market Cap

 Menene Market Cap, Kuma Me Yasa Yake Da Muhimmanci? A duniya kasuwancin kuɗi da crypto, ana yawan jin kalmar Market Cap — amma menene ainihin ma'anarsa, kuma me yasa yake da muhimmanci? A cikin wannan rubutu, za mu bincika wannan batu a sauƙaƙe. Menene Market Cap? Market Cap takaitaccen suna ne ga “Market Capitalization,” wanda ke nufin jimillar darajar wata kadara a kasuwa. Ana samun sa ta hanyar ninkawa farashin kowane kaya ko coin da adadin kayayyakin da ake da su a kasuwa. Ga wata sauƙaƙƙiyar hanya ta lissafinsa: Market Cap = Farashin Coin × Jimillar Coins da Ke Kasuwa Misali: Idan farashin wani coin ɗaya N500 ne, kuma akwai coins miliyan 2 masu circulation a kasuwa, to market cap ɗinsa zai zama: N500 × 2,000,000 = N1,000,000,000 Me Yasa Market Cap Yake Da Muhimmanci? 1. Auna Girman coins Kasuwa: Market cap yana ba da cikakken bayani game da girman wata kadara idan aka kwatanta da wasu. Idan aka ce coin ɗin A yana da market cap Naira biliyan 10, yayin da coin ɗin B yake da Nai...

WEB3 JOBS

 A yau, ci gaban intanet ya kawo sabon salo wanda ake kira “Web 3.0”, wanda ke bada damar kirkire-kirkire, kulla dangantaka tsakanin masu amfani, da kuma samar da sabbin hanyoyi na kasuwanci. Wannan sabon zamani na intanet yana buɗe kofar dama mai yawa a fannin ayyukan IT da fasaha, inda ake buƙatar kwararru masu ilimin blockchain, smart contracts, da kuma decentralized applications (dApps). Ga wasu muhimman bayanai game da ayyukan Web 3: 1. Fahimtar Web 3 Web 3 na nufin wani sabon yanayi na intanet da ke karkata zuwa tsarin da ba ya karkata a hannun kamfanoni guda, inda bayanai suke a rabe ta hanyar amfani da blockchain. Wannan tsarin yana bai wa masu amfani iko da bayanansu da kuma damar yin hulɗa kai tsaye ba tare da tsangwama ba. 2. Muhimman Ayyuka a Web 3  Blockchain Developers: Wannan rukuni na ayyuka ya shafi tsara da kuma gina tsarin blockchain da smart contracts. Kwararru masu amfani da programming language irin su Solidity ana buƙatarsu sosai.  dApp Engineers: ...

eNaira

eNaira, Digital money da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙirƙira, yana daga cikin sabbin hanyoyin inganta hada-hadar kuɗi a Nijeriya .An ƙaddamar da shine domin sauƙaƙe ma'amalolin Internet, rage caji da haɓaka tsaro a cikin tsarin kuɗi na Najeriya. Wannan tsarin zai taimaka wajen haɗa al'umma tare da kawo sauƙin amfani da kuɗi. Menene eNaira? eNaira Digital money ne da aka fitar ta hanyar CBN, wanda ke aiki kamar yadda kuɗaɗen gargajiya ke aiki, amma ta hanyar yanar gizo. Wannan tsarin zai baiwa 'yan Najeriya damar yin ma'amaloli cikin sauri, tsaro, da kuma sauƙin sarrafawa ba tare da buƙatar banki ba. Amfanin eNaira Saurin Ma'amala: zai baka damar yin ma'amaloli cikin sauri sosai, kuma zai rage ɓata lokaci da wahala wajen gudanar da kasuwanci. Tsaro: Tabbas kamar yanda bincike ya nuna eNaira zai bayar da kariya daga damfara da satar bayanai. Rage Caji: Yawanci, transactions da ake gudanarwa ta hanyar eNaira suna da ƙananan caji idan aka kwatanta da hanyoyin b...

Kana Bata Lokaci Da Yawa a social media ?

 Kana Bata Lokaci Da Yawa a social media ? Ga Yadda Zaka Rage Ɓata lokacin ka a social media. Wayoyin zamani suna da matukar amfani, amma kuma suna iya zama babbar hanyar ɓata lokaci— musamman idan ana ta faman biye-biyen social media . Idan kana ganin kana bata lokaci da yawa a kan wadannan manhajoji, ga wasu shawarwari da za su taimaka maka ka rage amfani da wayarka: 1. Bibiyar Lokacin da Kake Cinyewa: Yawancin wayoyi suna da fasalin in screen time tracking. A kan Android, Ka shiga setting> Digital Wellbeing & Parental Controls. A kan iPhone kuma, duba setting> Screen Time. Wannan zai taimaka maka wajen ganin inda lokacinka ke tafiya. 2. Amfani da time limit app: Yin amfani da app din iyakance amfani da apps. Misali, zaka iya sa iyaka na mintuna 30 ga manhajoji kamar Facebook ko TikTok(Ni mintina 5 na saka. Sai dai in sun ƙare in sake komawa). Idan ka cika wannan lokaci, za a toshe manhajar da zarar lokacin ya kare. 3. Turn off Notifications: Kashe Notifications da ba d...

An saki PAVEL DUROV

 A yau, 15 ga Maris, 2025, an bayar da rahoton cewa an saki Pavel Durov, wanda ya kafa kuma yake jagorantar manhajar saƙonnin nan ta Telegram, bayan da aka tsare shi a Faransa tun watan Agusta na shekarar 2024. An kama Durov ne bisa zargin cewa an yi amfani da dandamalin Telegram wajen aikata laifuka kamar safarar miyagun kwayoyi, yada hotunan cin zarafin yara, da kuma ayyukan ta'addanci.  Bayan kamun nasa, an tuhume shi da rashin yin aiki tare da hukumomin tsaro wajen hana irin waɗannan laifuka a kan dandamalin sa. An bayar da belinsa kan kuɗi har euro miliyan biyar, tare da sharuɗɗan cewa zai ci gaba da kasancewa a Faransa, ya kuma rika halartar ofishin 'yan sanda sau biyu a mako.  Sakin Durov ya haifar da martani daga masu amfani da Telegram da kuma masu goyon bayan 'yancin faɗar albarkacin baki, waɗanda suka nuna damuwa kan tasirin da kamun nasa zai iya yi kan 'yancin faɗi da kuma sirrin bayanai a intanet. A halin yanzu, Telegram na da kusan masu amfani miliyan 950 ...