Skip to main content

Market Cap

 Menene Market Cap, Kuma Me Yasa Yake Da Muhimmanci?


A duniya kasuwancin kuɗi da crypto, ana yawan jin kalmar Market Cap — amma menene ainihin ma'anarsa, kuma me yasa yake da muhimmanci? A cikin wannan rubutu, za mu bincika wannan batu a sauƙaƙe.



Menene Market Cap?


Market Cap takaitaccen suna ne ga “Market Capitalization,” wanda ke nufin jimillar darajar wata kadara a kasuwa. Ana samun sa ta hanyar ninkawa farashin kowane kaya ko coin da adadin kayayyakin da ake da su a kasuwa. Ga wata sauƙaƙƙiyar hanya ta lissafinsa:


Market Cap = Farashin Coin × Jimillar Coins da Ke Kasuwa


Misali: Idan farashin wani coin ɗaya N500 ne, kuma akwai coins miliyan 2 masu circulation a kasuwa, to market cap ɗinsa zai zama:


N500 × 2,000,000 = N1,000,000,000


Me Yasa Market Cap Yake Da Muhimmanci?


1. Auna Girman coins Kasuwa:

Market cap yana ba da cikakken bayani game da girman wata kadara idan aka kwatanta da wasu. Idan aka ce coin ɗin A yana da market cap Naira biliyan 10, yayin da coin ɗin B yake da Naira miliyan 500, hakan na nufin coin A ya fi girma a kasuwa.



2. Auna Hatsari da Tsaron Coins:

Coins da ke da babban market cap sukan fi karko, saboda akwai mutanen da suka zuba jari a cikinsa da yawa. A gefe guda, coins da ke da ƙaramin market cap sukan fi zama masu hatsari — amma kuma sun fi damar ba da riba da sauri.


Sau da yawa, coins da ke da ƙaramin market cap suna da damar haɓaka cikin sauri idan an samu yawan masu saka jari. Duk da haka, wannan yana zuwa da haɗari mai yawa.


Idan kana son saka jari, duba market cap yana taimakawa wajen yanke shawara mai kyau. Kada ka dogara da farashi kawai — domin wani coin na iya kasancewa da arha, amma yana da babbar market cap saboda yawan adadinsa a kasuwa.



Market cap yana da matukar muhimmanci a fahimtar yadda kasuwa ke aiki, da kuma yanke shawara mai kyau idan ana maganar saka jari. Duk wanda yake son yin kasuwanci da hikima, zai fi dacewa ya kalli market cap domin fahimtar yadda coins ke tafiya a kasuwa.


Ka tuna, zuba jari yana bukatar ilimi da hakuri. Kada ka yi gaggawa — ka yi bincike sosai kafin ka yanke shawara!


#MarketCap #Crypto #IliminKudi #Kasuwanci

Comments

Popular posts from this blog

WEB 3 opportunities

 Damar Makin Dake Cikin Web3 A yau, duniya na tunkarar sabon salo ta fuskar fasaha da tattalin arziki ta hanyar Web3 — wani sabon tsarin yanar gizo da ke amfani da fasahar blockchain don kawo cin gashin kai, tsaro, da gaskiya. A cikin wannan sabon yanayi, dama ta musamman ta bayyana a fannonin kasuwanci, aikin yi, da kirkire-kirkire. Ga wasu daga cikin damar makin da ke akwai: 1. Ciniki da Zuba Jari a Crypto Web3 ta bude kofa ga sababbin hanyoyin zuba jari kamar su: Futures Trading: Yin hasashen hauhawa ko faduwar darajar coins. Staking da Liquidity Providing: Samun riba ta hanyar bada gudummawa wajen tabbatar da amincin hanyoyin blockchain. 2. Content Creation Content creators suna da damar samar da content mai amfani kamar: Education: Bayar da ilimi akan amfani da crypto da dApps. NFTs: Samar da fasahohin dijital da za a iya siyarwa ko musayar su. 3. Kasuwanci da Cinikayya Akwai damar kafa kasuwanci da dama, irinsu: DeFi (Decentralized Finance): Bada lamuni ko karbar lamuni ba ta...

Entry and Exit Trigger

 Entry and Exit Triggers a Kasuwar Crypto Trading A kasuwar crypto trading, sanin entry da exit triggers yana da matukar muhimmanci don cin moriyar kasuwa ba tare da fadawa cikin asara ba. Entry trigger yana nufin lokacin da ya dace ka shiga kasuwa, yayin da exit trigger ke nufin lokacin da ya dace ka fita daga kasuwa don riba ko rage asara. Entry Triggers (Shiga Kasuwa) Entry trigger yana taimakawa wajen tabbatar da cewa ka shiga kasuwa a lokacin da ya dace. Ga wasu daga cikin abubuwan da za ka iya amfani da su don yanke shawarar shiga: 1. Technical Indicators Moving Averages (MA): Idan farashin ya keta sama da Moving Average (kamar 50 EMA ko 200 EMA), yana iya zama alamar bullish entry. Relative Strength Index (RSI): Idan RSI ya yi ƙasa da 30, yana iya nuna cewa kasuwa ta yi oversold kuma yana yiwuwa farashin ya tashi. MACD Crossover: Idan MACD line ya haye sama da signal line, yana iya nuna bullish entry. 2. Chart Patterns Breakout: Idan farashin ya karya wani key resistance lev...

Facebook Monetisation

 Facebook Monetization: Yadda Ake Samun Kuɗi a Facebook Facebook na daya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗi ga masu ƙirƙirar contents. Idan kana da shafi ko abun da kake ƙirƙira, zaka iya cin gajiyar hanyoyin monetization da Facebook ke bayarwa. 1. Hanyoyin Monetization a Facebook 1.1. In-Stream Ads (Talla a Bidiyo) Wannan hanya ce da ke ba masu bidiyo damar saka tallace-tallace a cikin bidiyonsu. Don zama eligible: Dole ne ka sami akalla mintuna 3,000 na kallo a cikin kwanaki 60 daga bidiyoyin ka na 3+ minutes. Dole ne ka sami mabiya 10,000 a shafin ka. Ana buƙatar shafin ka ya cika ka’idar Facebook Partner Monetization. 1.2. Facebook Stars Ana amfani da Facebook Stars don samun gudummawar kuɗi daga masu kallo yayin yawo da bidiyo kai tsaye (live streaming). 1.3. Subscriptions (Rajista) Masoya za su iya yin biyan kuɗi don samun content na musamman. Don zama eligible: Kana buƙatar mabiya 10,000 ko 5,000 followers + 250 returning viewers. Kana buƙatar samun 180,000 watch minutes ...