Skip to main content

Posts

Showing posts from April, 2025

Technical Indicators

  Mece Ce Technical Indicator a Cikin Trading? Technical indicators kayan aikin ne da traders ke amfani da su don nazarin motsin price a kasuwa. Suna taimaka wa trader su fahimci yanayin kasuwa—ko tana cikin bullish trend, bearish trend, ko sideways. Kamar Yadda Likita Ke Amfani da Thermometer don Duba Zafin Jiki, Trader na Amfani da Indicators don Duba Lafiyar Kasuwa. Manyan Nau’in Technical Indicators 1. Trend Indicators: Kamar irinsu:Moving Averages (MA), MACD  Su na taimakawa wajen gano inda kasuwa ke tafiya (uptrend ko downtrend). 2. Momentum Indicators: Misali kamar : RSI, Stochastic Oscillator Su na nuna ƙarfin motsin farashi da yiwuwar overbought ko oversold. 3. Volume Indicators: Misali Kamar: On-Balance Volume (OBV)  Su na nuna ƙarfin ciniki (trading volume) don tabbatar da motsin farashi. 4. Volatility Indicators: Misali kamar: Bollinger Bands  Su na auna yadda farashi ke canzawa da sauri ko jinkiri. Technical Indicators Suna taimaka wajen yanke shawarar s...

NFT Market Place

  Menene NFT Marketplace? NFT Marketplace wata kasuwa ce ta intanet da ake siyarwa da sayen abubuwan dijital da ake kira Non-Fungible Tokens (NFTs). Wannan kasuwa tana aiki ne da fasahar blockchain, wanda ke tabbatar da cewa mallakar kowane NFT ya tabbata ga mai shi na gaske. Yadda NFT Marketplace ke aiki A cikin irin wannan kasuwa, masu zane-zane, mawaka, masu bidiyo, da masu kirkirar abubuwan dijital na iya minting NFT — wato canza aikin su zuwa token a cikin blockchain kamar Ethereum ko Solana. Bayan hakan, suna iya saka shi a kasuwa domin a saya da cryptocurrency. Misali: Wani mai zane na iya daukar hotonsa, ya mint shi zuwa NFT a OpenSea, sannan ya saka farashi. Mai sha'awar hoton zai iya siyan wannan NFT ta amfani da crypto wallet kamar MetaMask. Abubuwan da zaka iya samu a NFT Marketplace Hotuna (Digital Art) Audio (waka, podcast) Bidiyo Game items (kayan cikin wasan kwamfuta) Domain names Mashahuran NFT Marketplaces 1. OpenSea – daya daga cikin manyan kasuwannin NFT a duniy...

Facebook Monetisation

 Facebook Monetization: Yadda Ake Samun Kuɗi a Facebook Facebook na daya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗi ga masu ƙirƙirar contents. Idan kana da shafi ko abun da kake ƙirƙira, zaka iya cin gajiyar hanyoyin monetization da Facebook ke bayarwa. 1. Hanyoyin Monetization a Facebook 1.1. In-Stream Ads (Talla a Bidiyo) Wannan hanya ce da ke ba masu bidiyo damar saka tallace-tallace a cikin bidiyonsu. Don zama eligible: Dole ne ka sami akalla mintuna 3,000 na kallo a cikin kwanaki 60 daga bidiyoyin ka na 3+ minutes. Dole ne ka sami mabiya 10,000 a shafin ka. Ana buƙatar shafin ka ya cika ka’idar Facebook Partner Monetization. 1.2. Facebook Stars Ana amfani da Facebook Stars don samun gudummawar kuɗi daga masu kallo yayin yawo da bidiyo kai tsaye (live streaming). 1.3. Subscriptions (Rajista) Masoya za su iya yin biyan kuɗi don samun content na musamman. Don zama eligible: Kana buƙatar mabiya 10,000 ko 5,000 followers + 250 returning viewers. Kana buƙatar samun 180,000 watch minutes ...

Yanda ake samun Airdrop mai kyau

  Yadda Ake Gano Airdrop Mai Kyau Airdrop na daya daga cikin hanyoyin da ake samun kudin crypto kyauta, amma ba duk airdrop ne suke ba da kuɗi ba. Wasu masu aidrops din scammers ne, yayin da wasu kuma na gaske ne. Don haka, yana da muhimmanci a san yadda ake tantance airdrop mai kyau domin gujewa fadawa cikin tarkon yan damfara. Ga wasu muhimman matakai da za ka bi: 1. Bincika Ingancin Project Shaharar Masu Project: Duba ko masu project din suna da kwarewa kuma an san su a fannin crypto. Shafin Yanar Gizo: Shin suna da shafin yanar gizo mai kyau da cikakken bayani? Whitepaper: Idan aikin yana da whitepaper, karanta shi don fahimtar manufar su da tsare-tsaren su. 2. Duba partnership da Use case na project  Idan manyan kamfanoni ko fitattun masu zuba jari suna goyon bayan ko tallafa wa project, hakan yana kara masa daraja. Duba ko yana da alaƙa da manyan kamfanonin blockchain kamar Binance, Ethereum Foundation, da sauransu. 3. Karanta Sharhin Jama’a da Ra’ayoyi A duba shafukan ...