Skip to main content

Yanda ake samun Airdrop mai kyau

 

Yadda Ake Gano Airdrop Mai Kyau


Airdrop na daya daga cikin hanyoyin da ake samun kudin crypto kyauta, amma ba duk airdrop ne suke ba da kuɗi ba. Wasu masu aidrops din scammers ne, yayin da wasu kuma na gaske ne. Don haka, yana da muhimmanci a san yadda ake tantance airdrop mai kyau domin gujewa fadawa cikin tarkon yan damfara. Ga wasu muhimman matakai da za ka bi:



1. Bincika Ingancin Project


Shaharar Masu Project: Duba ko masu project din suna da kwarewa kuma an san su a fannin crypto.


Shafin Yanar Gizo: Shin suna da shafin yanar gizo mai kyau da cikakken bayani?


Whitepaper: Idan aikin yana da whitepaper, karanta shi don fahimtar manufar su da tsare-tsaren su.



2. Duba partnership da Use case na project 


Idan manyan kamfanoni ko fitattun masu zuba jari suna goyon bayan ko tallafa wa project, hakan yana kara masa daraja.


Duba ko yana da alaƙa da manyan kamfanonin blockchain kamar Binance, Ethereum Foundation, da sauransu.



3. Karanta Sharhin Jama’a da Ra’ayoyi


A duba shafukan Reddit, Twitter, da Telegram domin ganin yadda mutane ke magana game da aikin.


Idan mutane da yawa suna korafi ko kokawa, yana da kyau a yi taka tsan-tsan.



4. Kauracewa Airdrop Mai Bukatar Bayanin Sirri


Kada ka bayar da private key na wallet ɗinka ga wani.


Kada ka haɗa wallet ɗinka da shafuka da ba a amince da su ba don gujewa kutse.



5. Duba Yanayin percentage din da zasu rabawa community din su 


Idan airdrop ya fitarwa community percent mai yawa fiye da yadda aka saba,to ka yi taka tsan-tsan.


Duba ko project ɗin na da roadmap da ke nuna tsawon lokacin da za a aiwatar da shi.



6. Rijista a Manyan Shafukan Airdrop


Don samun ingantattun airdrop, zaka iya duba shafuka kamar:


Airdrops.io


CoinMarketCap Airdrops


Earn by Coinbase


Binance Airdrop Page



7. Yin Amfani da Wallet Mai Tsaro


Yi amfani da Metamask ko Trust Wallet don karɓar airdrop.


Don gujewa zamba, zaka iya amfani da sabuwar wallet wacce ba ta da alaƙa da babban asusunka.



Samun kyautar crypto ta hanyar airdrop yana da kyau, amma yana da mahimmanci a bi matakan kariya domin gujewa fadawa Hannun scammers. Kafin ka Fara kowani airdrop, ka tabbatar da cewa project din yana da inganci, yana da manyan masu goyon baya, kuma ba ya bukatar bayananka na sirri. A koyaus

he, ka kasance mai lura da kuma kare asusunka daga scammers.


Comments

Popular posts from this blog

WEB 3 opportunities

 Damar Makin Dake Cikin Web3 A yau, duniya na tunkarar sabon salo ta fuskar fasaha da tattalin arziki ta hanyar Web3 — wani sabon tsarin yanar gizo da ke amfani da fasahar blockchain don kawo cin gashin kai, tsaro, da gaskiya. A cikin wannan sabon yanayi, dama ta musamman ta bayyana a fannonin kasuwanci, aikin yi, da kirkire-kirkire. Ga wasu daga cikin damar makin da ke akwai: 1. Ciniki da Zuba Jari a Crypto Web3 ta bude kofa ga sababbin hanyoyin zuba jari kamar su: Futures Trading: Yin hasashen hauhawa ko faduwar darajar coins. Staking da Liquidity Providing: Samun riba ta hanyar bada gudummawa wajen tabbatar da amincin hanyoyin blockchain. 2. Content Creation Content creators suna da damar samar da content mai amfani kamar: Education: Bayar da ilimi akan amfani da crypto da dApps. NFTs: Samar da fasahohin dijital da za a iya siyarwa ko musayar su. 3. Kasuwanci da Cinikayya Akwai damar kafa kasuwanci da dama, irinsu: DeFi (Decentralized Finance): Bada lamuni ko karbar lamuni ba ta...

Entry and Exit Trigger

 Entry and Exit Triggers a Kasuwar Crypto Trading A kasuwar crypto trading, sanin entry da exit triggers yana da matukar muhimmanci don cin moriyar kasuwa ba tare da fadawa cikin asara ba. Entry trigger yana nufin lokacin da ya dace ka shiga kasuwa, yayin da exit trigger ke nufin lokacin da ya dace ka fita daga kasuwa don riba ko rage asara. Entry Triggers (Shiga Kasuwa) Entry trigger yana taimakawa wajen tabbatar da cewa ka shiga kasuwa a lokacin da ya dace. Ga wasu daga cikin abubuwan da za ka iya amfani da su don yanke shawarar shiga: 1. Technical Indicators Moving Averages (MA): Idan farashin ya keta sama da Moving Average (kamar 50 EMA ko 200 EMA), yana iya zama alamar bullish entry. Relative Strength Index (RSI): Idan RSI ya yi ƙasa da 30, yana iya nuna cewa kasuwa ta yi oversold kuma yana yiwuwa farashin ya tashi. MACD Crossover: Idan MACD line ya haye sama da signal line, yana iya nuna bullish entry. 2. Chart Patterns Breakout: Idan farashin ya karya wani key resistance lev...

Facebook Monetisation

 Facebook Monetization: Yadda Ake Samun Kuɗi a Facebook Facebook na daya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗi ga masu ƙirƙirar contents. Idan kana da shafi ko abun da kake ƙirƙira, zaka iya cin gajiyar hanyoyin monetization da Facebook ke bayarwa. 1. Hanyoyin Monetization a Facebook 1.1. In-Stream Ads (Talla a Bidiyo) Wannan hanya ce da ke ba masu bidiyo damar saka tallace-tallace a cikin bidiyonsu. Don zama eligible: Dole ne ka sami akalla mintuna 3,000 na kallo a cikin kwanaki 60 daga bidiyoyin ka na 3+ minutes. Dole ne ka sami mabiya 10,000 a shafin ka. Ana buƙatar shafin ka ya cika ka’idar Facebook Partner Monetization. 1.2. Facebook Stars Ana amfani da Facebook Stars don samun gudummawar kuɗi daga masu kallo yayin yawo da bidiyo kai tsaye (live streaming). 1.3. Subscriptions (Rajista) Masoya za su iya yin biyan kuɗi don samun content na musamman. Don zama eligible: Kana buƙatar mabiya 10,000 ko 5,000 followers + 250 returning viewers. Kana buƙatar samun 180,000 watch minutes ...