Skip to main content

Facebook Monetisation

 Facebook Monetization: Yadda Ake Samun Kuɗi a Facebook



Facebook na daya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗi ga masu ƙirƙirar contents. Idan kana da shafi ko abun da kake ƙirƙira, zaka iya cin gajiyar hanyoyin monetization da Facebook ke bayarwa.


1. Hanyoyin Monetization a Facebook


1.1. In-Stream Ads (Talla a Bidiyo)


Wannan hanya ce da ke ba masu bidiyo damar saka tallace-tallace a cikin bidiyonsu. Don zama eligible:


Dole ne ka sami akalla mintuna 3,000 na kallo a cikin kwanaki 60 daga bidiyoyin ka na 3+ minutes.


Dole ne ka sami mabiya 10,000 a shafin ka.


Ana buƙatar shafin ka ya cika ka’idar Facebook Partner Monetization.



1.2. Facebook Stars


Ana amfani da Facebook Stars don samun gudummawar kuɗi daga masu kallo yayin yawo da bidiyo kai tsaye (live streaming).


1.3. Subscriptions (Rajista)


Masoya za su iya yin biyan kuɗi don samun content na musamman. Don zama eligible:


Kana buƙatar mabiya 10,000 ko 5,000 followers + 250 returning viewers.


Kana buƙatar samun 180,000 watch minutes a cikin kwanaki 60.



1.4. Affiliate Marketing


Kana iya sayar da kayayyaki ta hanyar haɗin gwiwa da kamfanoni daban-daban sannan a baka kaso daga ribar da aka samu.


1.5. Facebook Reels Play Bonus


Facebook yana biyan masu ƙirƙirar content idan reels ɗinsu sun samu views mai yawa.


2. Yadda zaka gane cewar ka zama Eligible 


Ka shiga Facebook Creator Studio


Ka duba Monetization eligibility don ganin ko ka cika ka'idojin.



3. Abubuwan Da Za Su Hana Monetization


Yin amfani da content da ba naka ba.


Karya dokokin Facebook.



Rashin yawan mabiya ko yawan kallon bidiyo.





Comments

Popular posts from this blog

WEB 3 opportunities

 Damar Makin Dake Cikin Web3 A yau, duniya na tunkarar sabon salo ta fuskar fasaha da tattalin arziki ta hanyar Web3 — wani sabon tsarin yanar gizo da ke amfani da fasahar blockchain don kawo cin gashin kai, tsaro, da gaskiya. A cikin wannan sabon yanayi, dama ta musamman ta bayyana a fannonin kasuwanci, aikin yi, da kirkire-kirkire. Ga wasu daga cikin damar makin da ke akwai: 1. Ciniki da Zuba Jari a Crypto Web3 ta bude kofa ga sababbin hanyoyin zuba jari kamar su: Futures Trading: Yin hasashen hauhawa ko faduwar darajar coins. Staking da Liquidity Providing: Samun riba ta hanyar bada gudummawa wajen tabbatar da amincin hanyoyin blockchain. 2. Content Creation Content creators suna da damar samar da content mai amfani kamar: Education: Bayar da ilimi akan amfani da crypto da dApps. NFTs: Samar da fasahohin dijital da za a iya siyarwa ko musayar su. 3. Kasuwanci da Cinikayya Akwai damar kafa kasuwanci da dama, irinsu: DeFi (Decentralized Finance): Bada lamuni ko karbar lamuni ba ta...

Entry and Exit Trigger

 Entry and Exit Triggers a Kasuwar Crypto Trading A kasuwar crypto trading, sanin entry da exit triggers yana da matukar muhimmanci don cin moriyar kasuwa ba tare da fadawa cikin asara ba. Entry trigger yana nufin lokacin da ya dace ka shiga kasuwa, yayin da exit trigger ke nufin lokacin da ya dace ka fita daga kasuwa don riba ko rage asara. Entry Triggers (Shiga Kasuwa) Entry trigger yana taimakawa wajen tabbatar da cewa ka shiga kasuwa a lokacin da ya dace. Ga wasu daga cikin abubuwan da za ka iya amfani da su don yanke shawarar shiga: 1. Technical Indicators Moving Averages (MA): Idan farashin ya keta sama da Moving Average (kamar 50 EMA ko 200 EMA), yana iya zama alamar bullish entry. Relative Strength Index (RSI): Idan RSI ya yi ƙasa da 30, yana iya nuna cewa kasuwa ta yi oversold kuma yana yiwuwa farashin ya tashi. MACD Crossover: Idan MACD line ya haye sama da signal line, yana iya nuna bullish entry. 2. Chart Patterns Breakout: Idan farashin ya karya wani key resistance lev...