Skip to main content

eNaira



eNaira, Digital money da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙirƙira, yana daga cikin sabbin hanyoyin inganta hada-hadar kuɗi a Nijeriya .An ƙaddamar da shine domin sauƙaƙe ma'amalolin Internet, rage caji da haɓaka tsaro a cikin tsarin kuɗi na Najeriya. Wannan tsarin zai taimaka wajen haɗa al'umma tare da kawo sauƙin amfani da kuɗi.



Menene eNaira?


eNaira Digital money ne da aka fitar ta hanyar CBN, wanda ke aiki kamar yadda kuɗaɗen gargajiya ke aiki, amma ta hanyar yanar gizo. Wannan tsarin zai baiwa 'yan Najeriya damar yin ma'amaloli cikin sauri, tsaro, da kuma sauƙin sarrafawa ba tare da buƙatar banki ba.


Amfanin eNaira


Saurin Ma'amala: zai baka damar yin ma'amaloli cikin sauri sosai, kuma zai rage ɓata lokaci da wahala wajen gudanar da kasuwanci.


Tsaro: Tabbas kamar yanda bincike ya nuna eNaira zai bayar da kariya daga damfara da satar bayanai.


Rage Caji: Yawanci, transactions da ake gudanarwa ta hanyar eNaira suna da ƙananan caji idan aka kwatanta da hanyoyin banki na gargajiya.


Sauƙin Samun Kuɗi: 'Yan Najeriya zamu iya samun sauƙin aikawa da karɓar kuɗi a ko’ina cikin ƙasar nan ba tare da wahala ba.


Sai dai akwai ƙalubale


Kalubale na Farkon da aka samu shine: farkon ƙaddamar da eNaira, wasu 'yan ƙasa sun nuna rashin fahimta ko jinkiri wajen amfani da tsarin. Wannan ya sa akwai buƙatar ƙarin wayar da kai da horaswa ga mutane.


Tsaro da Kariya: Duk da cewa tsarin yana da ingantaccen tsaro, CBN na ci gaba da ƙoƙarin inganta matakan tsaro domin kare bayanan masu amfani daga duk wani hari na yanar gizo.


Tallafawa daga Hukumomi: CBN na aiki tare da sauran hukumomi don inganta tsarin, ta yadda za a samu ci gaba a amfani da eNaira a fannoni daban-daban na tattalin arziki.


eNaira zai taka muhimmiyar rawa wajen sauya tsarin kuɗi a Najeriya, musamman a wannan zamani na Digital era damuke ciki. Idan aka inganta ilimi da wayar da kai a tsakanin jama'a, tare da ci gaba da inganta tsaro, eNaira na iya zama ginshiki a cikin tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasar. Hakan zai taimaka wajen rage dogaro ga tsare-tsaren banki na gargajiya, tare da baiwa masu amfani damar gudanar da harkokinsu cikin sauƙi da tsaro.


eNaira wata babbar nasara ce a fannin Digital money a Najeriya. Duk da cikas na farko, tsarin na ci gaba da samun karbuwa da inganci a tsakanin al’umma. Idan aka ci gaba da inganta matakan ilimi da tsaro, eNaira zai taimaka wajen sauƙaƙe ma'amaloli da haɓaka tattalin arzik

in ƙasar a cikin sauƙi.





Comments

Popular posts from this blog

WEB 3 opportunities

 Damar Makin Dake Cikin Web3 A yau, duniya na tunkarar sabon salo ta fuskar fasaha da tattalin arziki ta hanyar Web3 — wani sabon tsarin yanar gizo da ke amfani da fasahar blockchain don kawo cin gashin kai, tsaro, da gaskiya. A cikin wannan sabon yanayi, dama ta musamman ta bayyana a fannonin kasuwanci, aikin yi, da kirkire-kirkire. Ga wasu daga cikin damar makin da ke akwai: 1. Ciniki da Zuba Jari a Crypto Web3 ta bude kofa ga sababbin hanyoyin zuba jari kamar su: Futures Trading: Yin hasashen hauhawa ko faduwar darajar coins. Staking da Liquidity Providing: Samun riba ta hanyar bada gudummawa wajen tabbatar da amincin hanyoyin blockchain. 2. Content Creation Content creators suna da damar samar da content mai amfani kamar: Education: Bayar da ilimi akan amfani da crypto da dApps. NFTs: Samar da fasahohin dijital da za a iya siyarwa ko musayar su. 3. Kasuwanci da Cinikayya Akwai damar kafa kasuwanci da dama, irinsu: DeFi (Decentralized Finance): Bada lamuni ko karbar lamuni ba ta...

Entry and Exit Trigger

 Entry and Exit Triggers a Kasuwar Crypto Trading A kasuwar crypto trading, sanin entry da exit triggers yana da matukar muhimmanci don cin moriyar kasuwa ba tare da fadawa cikin asara ba. Entry trigger yana nufin lokacin da ya dace ka shiga kasuwa, yayin da exit trigger ke nufin lokacin da ya dace ka fita daga kasuwa don riba ko rage asara. Entry Triggers (Shiga Kasuwa) Entry trigger yana taimakawa wajen tabbatar da cewa ka shiga kasuwa a lokacin da ya dace. Ga wasu daga cikin abubuwan da za ka iya amfani da su don yanke shawarar shiga: 1. Technical Indicators Moving Averages (MA): Idan farashin ya keta sama da Moving Average (kamar 50 EMA ko 200 EMA), yana iya zama alamar bullish entry. Relative Strength Index (RSI): Idan RSI ya yi ƙasa da 30, yana iya nuna cewa kasuwa ta yi oversold kuma yana yiwuwa farashin ya tashi. MACD Crossover: Idan MACD line ya haye sama da signal line, yana iya nuna bullish entry. 2. Chart Patterns Breakout: Idan farashin ya karya wani key resistance lev...

Facebook Monetisation

 Facebook Monetization: Yadda Ake Samun Kuɗi a Facebook Facebook na daya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗi ga masu ƙirƙirar contents. Idan kana da shafi ko abun da kake ƙirƙira, zaka iya cin gajiyar hanyoyin monetization da Facebook ke bayarwa. 1. Hanyoyin Monetization a Facebook 1.1. In-Stream Ads (Talla a Bidiyo) Wannan hanya ce da ke ba masu bidiyo damar saka tallace-tallace a cikin bidiyonsu. Don zama eligible: Dole ne ka sami akalla mintuna 3,000 na kallo a cikin kwanaki 60 daga bidiyoyin ka na 3+ minutes. Dole ne ka sami mabiya 10,000 a shafin ka. Ana buƙatar shafin ka ya cika ka’idar Facebook Partner Monetization. 1.2. Facebook Stars Ana amfani da Facebook Stars don samun gudummawar kuɗi daga masu kallo yayin yawo da bidiyo kai tsaye (live streaming). 1.3. Subscriptions (Rajista) Masoya za su iya yin biyan kuɗi don samun content na musamman. Don zama eligible: Kana buƙatar mabiya 10,000 ko 5,000 followers + 250 returning viewers. Kana buƙatar samun 180,000 watch minutes ...