Skip to main content

Kana Bata Lokaci Da Yawa a social media ?

 Kana Bata Lokaci Da Yawa a social media ? Ga Yadda Zaka Rage Ɓata lokacin ka a social media.


Wayoyin zamani suna da matukar amfani, amma kuma suna iya zama babbar hanyar ɓata lokaci— musamman idan ana ta faman biye-biyen social media . Idan kana ganin kana bata lokaci da yawa a kan wadannan manhajoji, ga wasu shawarwari da za su taimaka maka ka rage amfani da wayarka:



1. Bibiyar Lokacin da Kake Cinyewa:

Yawancin wayoyi suna da fasalin in screen time tracking. A kan Android, Ka shiga setting> Digital Wellbeing & Parental Controls. A kan iPhone kuma, duba setting> Screen Time. Wannan zai taimaka maka wajen ganin inda lokacinka ke tafiya.



2. Amfani da time limit app:

Yin amfani da app din iyakance amfani da apps. Misali, zaka iya sa iyaka na mintuna 30 ga manhajoji kamar Facebook ko TikTok(Ni mintina 5 na saka. Sai dai in sun ƙare in sake komawa). Idan ka cika wannan lokaci, za a toshe manhajar da zarar lokacin ya kare.



3. Turn off Notifications:

Kashe Notifications da ba dole ba domin rage kwadayin duba waya duk lokacin da ta yi kara ko walƙiya.



4. Use focus mode 

A kunna Focus Mode a kan Android ko Do Not Disturb a kan iPhone lokacin aiki ko karatu. Wannan yana hana shigowar sanarwar sada zumunta, yana ba ka damar mai da hankali.



5. Cire Manhajojin Sada Zumunta Daga Fuskantar Farko:

Idan ba ka ga manhajar ba, ba za ka tuna da ita ba! Matsar da manhajojin sada zumunta zuwa wani fayil a gefe, ko ka cire su daga saman Home screen din ka.



6. Maye Gurbin da kake latsa waya da wani abu mai amfani:

Duk lokacin da ka ji kana son shiga social media, maye gurbin hakan da wata hanya mai amfani — kamar karanta wani gajeren labari, koyon wani sabon abu,ko yin atisaye na tunani (mindfulness).



7. Use apps that help you focus :

Akwai manhajoji kamar Forest, Freedom, ko Stay Focused da za su iya toshe manhajojin sada zumunta na ɗan wani lokaci, suna ba ka damar aiki ba tare da tangarda ba.


Daga karshe:

Ka yi kokari ka zama mai sarrafa wayarka, ba ita ce ke sarrafa ka ba. Ta hanyar kafa iyakoki da yin amfani da fasaha cikin hankali, zaka iya mayar da hankalinka kan a

bubuwan da suka fi muhimmanci.



Comments

Popular posts from this blog

WEB 3 opportunities

 Damar Makin Dake Cikin Web3 A yau, duniya na tunkarar sabon salo ta fuskar fasaha da tattalin arziki ta hanyar Web3 — wani sabon tsarin yanar gizo da ke amfani da fasahar blockchain don kawo cin gashin kai, tsaro, da gaskiya. A cikin wannan sabon yanayi, dama ta musamman ta bayyana a fannonin kasuwanci, aikin yi, da kirkire-kirkire. Ga wasu daga cikin damar makin da ke akwai: 1. Ciniki da Zuba Jari a Crypto Web3 ta bude kofa ga sababbin hanyoyin zuba jari kamar su: Futures Trading: Yin hasashen hauhawa ko faduwar darajar coins. Staking da Liquidity Providing: Samun riba ta hanyar bada gudummawa wajen tabbatar da amincin hanyoyin blockchain. 2. Content Creation Content creators suna da damar samar da content mai amfani kamar: Education: Bayar da ilimi akan amfani da crypto da dApps. NFTs: Samar da fasahohin dijital da za a iya siyarwa ko musayar su. 3. Kasuwanci da Cinikayya Akwai damar kafa kasuwanci da dama, irinsu: DeFi (Decentralized Finance): Bada lamuni ko karbar lamuni ba ta...

Entry and Exit Trigger

 Entry and Exit Triggers a Kasuwar Crypto Trading A kasuwar crypto trading, sanin entry da exit triggers yana da matukar muhimmanci don cin moriyar kasuwa ba tare da fadawa cikin asara ba. Entry trigger yana nufin lokacin da ya dace ka shiga kasuwa, yayin da exit trigger ke nufin lokacin da ya dace ka fita daga kasuwa don riba ko rage asara. Entry Triggers (Shiga Kasuwa) Entry trigger yana taimakawa wajen tabbatar da cewa ka shiga kasuwa a lokacin da ya dace. Ga wasu daga cikin abubuwan da za ka iya amfani da su don yanke shawarar shiga: 1. Technical Indicators Moving Averages (MA): Idan farashin ya keta sama da Moving Average (kamar 50 EMA ko 200 EMA), yana iya zama alamar bullish entry. Relative Strength Index (RSI): Idan RSI ya yi ƙasa da 30, yana iya nuna cewa kasuwa ta yi oversold kuma yana yiwuwa farashin ya tashi. MACD Crossover: Idan MACD line ya haye sama da signal line, yana iya nuna bullish entry. 2. Chart Patterns Breakout: Idan farashin ya karya wani key resistance lev...

Facebook Monetisation

 Facebook Monetization: Yadda Ake Samun Kuɗi a Facebook Facebook na daya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗi ga masu ƙirƙirar contents. Idan kana da shafi ko abun da kake ƙirƙira, zaka iya cin gajiyar hanyoyin monetization da Facebook ke bayarwa. 1. Hanyoyin Monetization a Facebook 1.1. In-Stream Ads (Talla a Bidiyo) Wannan hanya ce da ke ba masu bidiyo damar saka tallace-tallace a cikin bidiyonsu. Don zama eligible: Dole ne ka sami akalla mintuna 3,000 na kallo a cikin kwanaki 60 daga bidiyoyin ka na 3+ minutes. Dole ne ka sami mabiya 10,000 a shafin ka. Ana buƙatar shafin ka ya cika ka’idar Facebook Partner Monetization. 1.2. Facebook Stars Ana amfani da Facebook Stars don samun gudummawar kuɗi daga masu kallo yayin yawo da bidiyo kai tsaye (live streaming). 1.3. Subscriptions (Rajista) Masoya za su iya yin biyan kuɗi don samun content na musamman. Don zama eligible: Kana buƙatar mabiya 10,000 ko 5,000 followers + 250 returning viewers. Kana buƙatar samun 180,000 watch minutes ...