A yau, ci gaban intanet ya kawo sabon salo wanda ake kira “Web 3.0”, wanda ke bada damar kirkire-kirkire, kulla dangantaka tsakanin masu amfani, da kuma samar da sabbin hanyoyi na kasuwanci. Wannan sabon zamani na intanet yana buɗe kofar dama mai yawa a fannin ayyukan IT da fasaha, inda ake buƙatar kwararru masu ilimin blockchain, smart contracts, da kuma decentralized applications (dApps). Ga wasu muhimman bayanai game da ayyukan Web 3:
1. Fahimtar Web 3
Web 3 na nufin wani sabon yanayi na intanet da ke karkata zuwa tsarin da ba ya karkata a hannun kamfanoni guda, inda bayanai suke a rabe ta hanyar amfani da blockchain. Wannan tsarin yana bai wa masu amfani iko da bayanansu da kuma damar yin hulɗa kai tsaye ba tare da tsangwama ba.
2. Muhimman Ayyuka a Web 3
Blockchain Developers: Wannan rukuni na ayyuka ya shafi tsara da kuma gina tsarin blockchain da smart contracts. Kwararru masu amfani da programming language irin su Solidity ana buƙatarsu sosai.
dApp Engineers: Su ne ke gina decentralized applications (dApps) wanda suke amfani da blockchain don bada services and products to users.
Cybersecurity specialist : Domin ba da tsaro. kwararrun masu kula da tsaro na intanet( cybersecurity specialist) suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron bayanai da kuma kare harin Hackers.
Data Analyst da Blockchain Analysts: Waɗannan kwararrun suna nazarin bayanai a cikin tsarin blockchain, suna fitar da bayanai masu mahimmanci don taimakawa kamfanoni wajen yanke shawara.
3. Skills da ake Bukata
Don samun nasara a fannin Web 3 jobs, akwai wasu fasahohi da ake buƙata:
Ilmin Blockchain da Cryptography: Fahimtar yadda tsarin blockchain ke aiki da kuma dabarun tsaro na zamani.
Programming language : Misali Solidity, Rust, da JavaScript suna daga cikin manyan Programming languages da ake amfani da su wajen haɓaka dApps.
Ƙwarewa a Tsarin Cloud da Distributed Systems: Domin gina tsarin da zai iya aiki a yanayi daban-daban ba tare da dogaro da cibiyar ba
yanai guda ɗaya ba.

Comments
Post a Comment